Connect with us

News

Zamu Tabbatar Da Jagoranci Na Gari, Ba Tare Da Son Zuciya Ba – Falgore

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Shugaban majalisar dokokin Kano Jibril Isma’il Falgore ya ce zai yi kokari wajen rike amanar da aka dora masa, da kuma cika alkawarin da ya daukarwa al’ummar da yake wakilta da jihar Kano baki daya.

 

Advertisement

Jibril Falgore, ya bayyana hakane yayin ziyarar da ya kai yankin Falgore ranar Asabar dake cikin Karamar hukumar Tudun Wada.

Tinubu Ya Rushe Dukkan Hukumomin Gudanarwar Ma’aikatu Da Hukumomin Gwamnati

Ya ce zai hada kai da sauran ‘yan majalisar dokokin Kano, don taimakawa gwamnati domin cimma manufofin ta na ci gaba.

Advertisement

 

Jibril Isma’il Falgore, ya kuma godewa al’ummar karamar hukumar Rogo bisa yadda suka bashi hadin kai har ya kai ga cimma nasara.

Advertisement

 

A nasa jawabi guda cikin shugabanin jam’iyar NNPP a karamar hukumar Rogo Ibrahim Haruna Zoza, ya nuna godiyar sa ga ‘yan majalisar dokokin Kano bisa yadda suka zabi Jibril Isma’il Falgore, a matsayin shugaban majalisar.

Advertisement

Ya kuma bukaci shugaban majalisar da shige gaba wajen gyara hanyoyin karamar hukumar da suka lalace.

Ibrahim Haruna Zoza, ya kuma ce suna da yakinin gwamnatin Abba Kabir Yusuf zata ceto jihar Kano daga matsalolin da take fuskanta

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending