Connect with us

News

An Rusau a Kano ne domin ramuwar gayya.– Tsohon Dan Takarar Gwamna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano, Sani Bello, ya ce aikin rusau da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi, an yi shi ne domin ramuwar gayya.

Advertisement

Bello ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s a shirin  Politics Today.

Shugaba kasa  Tinubu ya amince da rusa shuwagabannin hukumomin gwamnatin tarayya.

Ya ce, “Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bai koyi darasi daga gwamnatin da ta gabata ba a lokacin da yake gudanar da aikin rusasshe. Wasu mutane sun garzaya kotu kuma gwamnatin jihar ta baiwa wani mutum guda sama da Naira miliyan 500 a Farm Centre.

Advertisement

“A cewar rahoton kasar an lalata sama da Naira biliyan 129 a atisayen. Rugujewar abin tunawa da Kano shi ne ya sa aikin ya fito fili. An yi shi ne saboda ramuwar gayya da fushi.

“Lokacin da za a yanke shawarar da za ta shafi wasu ‘yan jihar, ya kamata a yi wani matakin Jan hankali. Rushe wani katafaren tarihi na Kano da aka gina domin murnar cika shekaru 50 da kafa jihar Kano, ya nuna cewa akwai fushi da gaggawar gudanar da wadannan atisayen don kawai ganin an kawar da abubuwan da gwamnatin da ta shude ta yi a baya a jihar. ”

Advertisement

Sai dai da yake mayar da martani ga sakataren gwamnatin jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, ya ce an gudanar da aikin ne domin cika alkawuran da gwamnatin ta dauka a yakin neman zabe.

Ya ce gwamnati na aiki tukuru domin kwato dukkan filayen da gwamnatin Ganduje ta sayar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending