News
Na samu goran gayyata na musamnan daga Majalisar dinkin duniya – Malam Shekarau.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya samu wani goron gayyata na musamman daga sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya zuwa birnin New York dake Amurka.
Malam Shekarau yace ba’a bashi cikakken bayani kan dalilin gayyatar ba, amma zai amsa gayyatar a mako mai zuwa.
A wani sako da mai taimakawa tsohon gwamnan kan kafafen sada zumunta da daukar hoto Jibril Muhammad Na-Tara ya wallafa ya tabbatar da wannan goron gayyata da aka aikewa tsohon gwamnan na Kano Malam Ibrahim Shekarau.
Yan ta’adda sun nemi kudin fansa N25m na daliban Zamfara da aka sace
Premier Radio 102.7 FM ta rawaito cewa Tunda fari dai anta yada cewa majalisar dinkin duniya zata bawa tsohon gwamnan na Kano mukami, to sai dai Malam Ibrahim Shekarau yace gayyatarshi sakatare janar yayi, kuma shi kanshi bashi da cikakken bayanin dalilin gayyatar da majalisar dinkin duniya ta masa.
Advertisements
