Connect with us

News

Yan sandan da suka taka mutum da mota na fuskantar hukunci a Najeriya

Published

on

AIG Olukayode Egbetokun/FACEBOOKCopyright: AIG Olukayode Egbetokun/FACEBOOK ...

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya na riƙo, Olukayode Egbetokun, ya ce ‘yan sandan da ake zargi da taka wani mutum da mota lokacin da yake ɗaure da ankwa a jihar Edo, suna fuskantar ladabtarwa.

Advertisement

An Fuskanci Wani Yanayin Zafi Na Tarihi Ranar Talata A Kasashen Duniya

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, bayan ‘yan sanda sun taka shi da motarsu ne, sai kuma suka yi ta jan sa a ƙasa a kan titin Ekpoma na jihar Edo.

Advertisement

An ce lamarin ya haifar da fargaba da tunzuri a yankin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Babban Sufeton ya sammaci ‘yan sandan da suka aikata wannan abu zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Advertisement

Sai dai kuma wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar ranar Alhamis ta ce Babban Sufeto ya bayar da umarnin rushe ayarin ƴan sandan a jihar.

Sanarwar ta ce, “A wani namijin yunƙuri don magance rashin ɗa’ar da wasu ‘yan sanda suka aikata a rundunar ‘yan sandan Edo ta hanyar taka wani ɗan ƙasa da mota a Ekpoma, muƙaddashin babban sufeton na Najeriya ya dauki matakin rusa ayarin ‘yan sandan nan take.”

Advertisement

“Wannan matakin na da nufin daidaita zaman ‘yan sanda a jihar da ƙarfafa gwiwar jama’a ta yadda za su sake yarda da ‘yan sanda.”

Ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin nuna cewa rundunar ta yi Allah-wadai da irin wannan hali.

Advertisement

BBC

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending