News
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya amince da nadin mutane 15 a matsayin masu ba da shawara na musamman kan fannoni daban-daban.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin mutane 15 a matsayin masu ba da shawara na musamman kan fannoni daban-daban.
Wadanda aka nada sun hada da Hon. Isyaku Ali Danja, mai ba da shawara na musamman kan harkokin majalisan da Hon. Muhammad Jamu Yusuf, mai ba da shawara na musamman kan hulda da jama’a na kasa da kasa da kuma Col. Abubakar Usman Garin Malam mai ritaya Mashawarci na Musamman kan kare Iftila’oi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Sanarwar ta ce sauran sun hada da Malam Usamatu Salga, mai ba da shawara na musamman kan harkokin addinai da Hon. Abduljabbar Muhammad Umar , mai ba da shawara na musamman kan harkokin zuba jari da hadin gwiwar bangarori masu zaman kansu da Hon. Aminu Abba Ibrahim, mai ba da shawara na musamman kan ma’adanai da kuma Injiniya Nura Hussain, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasuwanci.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
