News
Rundunar ‘Yan sanda jahar Bauchi sun kashe masu garkuwa da mutane biyu tare da ceto mutum 10
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce ta kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da ceto mutum 10 da akayi garkuwa da su a wani samame da ta kai a karamar hukumar Ningi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Auwal Musa Muhammad ne bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ‘yan sandan da ke kan titin Yandoka a ranar Talata.
Wasan farko da ‘yar kwallo mai sa hijabi ta buga a Gasar Cin Kofin Duniya
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa an yi ta yin garkuwa da mutane ba tare da kakkautawa ba a karamar hukumar Ningi, wanda ake kaiwa manoma wadanda a yanzu ke fargabar zuwa gonakinsu.
CP ya ce an gudanar da aikin ceton ne tare da hadin gwiwar mafarauta.
Daya daga cikin nasarar da aka samu a tsakanin ranakun 17 zuwa 20 ga watan Yuli, jami’an sun ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba tare da sada su da iyalansu.
Hakazalika, ‘yan sanada sun kai farmaki kan ‘yan ta’addan tare da kashe biyu daga cikin masu garkuwa da mutane tare da kama daya, yayin da sauran ‘yan yan sandan suka samu nasarar fatattakar su a yayin wani artabu da jami’ai
