Connect with us

News

Abubuwan da suka kamata ku sani game da juyin mulkin A Jamhuriyar Nijar.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Wasu sojoji da ke tsaron fadar shugaban kasa sun tabbatar cewa, lallai sun kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum kamar yadda suka sanar kai-tsaye a gidan talabijin na kasa, yayin da kasashen duniya ke ta mayar da martani kan wannan al’amari.

Mai magana da yawun sojojin, Kanar Manjo Amadou Abdramane ya ce, jami’an tsaro sun yanke shawarar kawo karshen gwamnatin saboda tabarbarewar tsaro da kuma koma-bayan more rayuwa da tattalin arziki a cewarsa.

Advertisement

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan jinkai a Nijar bayan juyin mulki

Kazalika sojojin sun ce, sun rufe daukacin kan iyakokin kasar tare da kafa dokar hana zirga-zirga a fadin kasar, baya ga dakatar da dukkanin cibiyoyin gwamnati.

 

Advertisement

Akwai dai kimanin sojoji tara da ke tsaye a bayan Abdramane a lokacin da yake sanar da kifar da gwamnatin shugaba Bazoum ta kafar talabijin din.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kawo yanzu babu masaniya game da halin da shugaba Bazoum ke ciki, lamarin da ya kara jefa fargaba a zukatan jama’a a ciki da wajen kasar.

Advertisement

 

Wannan na zuwa ne bayan da sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar sun tsare Bazoum na wasu ‘yan sa’o’i kafin daga bisani su sanar da yi masa juyin mulki.

Advertisement

 

Ministan harkokin waje yayi watsi da ikirarin juyin mulki

Advertisement

 

Yayin zantarwarsa da tasahar talabijin ta France24, ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi Massaoudou, ya ce har yanzu Mohamed Bazoum ne shugaban kasar.

Advertisement

 

Minista Massaoudou, ya kuma bukaci sojojin da ke da hannu a wannan lamari da su gaggauta komawa a cikin barikokinsu.

Advertisement

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Kasashen Turai EU da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS sun yi Allah-wadai da abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.

 

Advertisement

A cikin kakkausar lafazi, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya caccaki yunkurin juyin mulkin da ya bayyana a matsayin zagon-kasa ga gwamnatin demokuradiya da kuma sukurkuta zaman lafiyar kasar.

 

Advertisement

Guterres ya yi kira ga dukkanin masu hannu a wannan yunkurin na juyin mulki da su janye matakinsu domin kare dokokin kundin tsarin mulki.

 

Advertisement

Ita ma fadar White House ta shugaban Amurka ta ce tana cikin damuwa kan abin da ke faruwa a Nijar, inda ta yi tur da tsare shugaba Bazoum tare da jan kunnen dakarun suka tsare shi da su gaggauta sakin sa domin kauce wa tashin hankali a kasar.

 

Advertisement

Haka nan Kungiyar Kasashen Turai ta EU ta bakin shugaban kula da manufofinta na ketare, Josep Borrell ta caccaki abin da ta kira yunkurin wargaza demokuradiya da kuma barazana ga zaman lafiyar Nijar.

Tuni Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ta nada shugaban Benin, Patrice Talon domin jagorantar wata tawaga ta musamman da aka kafa domin shiga tsakanin bangarorin biyu da zummar sasanta rikicin na juyin mulki.

Advertisement

 

ECOWAS ta nanata cewa, ba za ta lamunci ci gaba da samun juye-juyen mulki ba a kasashen Afrika ta yamma.

Advertisement

 

Shugaba Bazoum wanda amini ne na kut da kut da Faransa, an zabe shi ne a shekarar 2021 domin jagorantar kasar da ke fama da talauci, yayin da take da tarihin samun rashin zaman lafiya.

Advertisement

 

Nijar ta gamu da juye-juyen mulki har sau hudu tun bayan karbar ‘yancinta daga Faransa a shekarar 1960 baya ga dimbin yunkuri iri-iri da aka yi na kifar da wasu shugabannin kasar daga kan karaga.

Advertisement

 

Tun daga shekarar 2020, an samu akalla juyin mulki har sau biyar a wasu kasashen yammacin Afrika.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending