News
Babu Wani Umarni Da Muka Samu Kan Shirin Fara Afkawa Sojojin Juyin Mulkin Nijar – Sojojin Najeriyaa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Rundunar sojin kasar nan ta ce har yanzu ba ta samu wani umarni ba na fara daukar matakin soji, kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana haka a yau a lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoton yanar gizo dake cewa rundunar na shirya dakarunta domin daukar matakin soji a Jamhuriyar Nijar.
Sojojin sama sun yi luguden wuta kan manyan yan bindigar da suka addabi jihar Katsina da Zamfara
Janar Gusau yace matakin amfani da karfin sojoji shine mataki na karshe da ya kamata a dauka kan al’amarin idan duk wani zabi ya gaza a tattaunawa da masu yunkurin juyin mulki da kuma mayar da gwamnatin Jamhuriyar Nijar kan tsarin mulki.
Ya yi nuni da cewa, rundunar sojin Najeriya ba za ta iya ci gaba da yin shiri da kowace kasa ta ECOWAS ba, ba tare da izini daga hukumomin shugabannin kasashe da gwamnatoci ba.
