Connect with us

News

Jihar Kano Na Bukatar Naira Biliiyan 6 Domin Samar Da Kujeru A Makarantu – Doguwa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Kwamishinan ilimi, Alhaji Umar Doguwa, ya ce jihar Kao na bukatar Naira biliyan 6 don samar da kujerun zama ga daliban makarantun firamare da sakandare.

Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an asusun tallafawa kananan yara na majalissar dinkin duniya UNICEF, ofishin dake kula da Kano, karkashin jagorancin Rahama Rihood Mohammad Farah, a ofishinsa.

Advertisement

Babu Wani Umarni Da Muka Samu Kan Shirin Fara Afkawa Sojojin Juyin Mulkin Nijar – Sojojin Najeriyaa

A cewar Doguwa, mafi akasarin yara miliyan 5.2 da ke makarantun Kano ba su da kujeru da tebura, inda ya ce a wata makaranta da ke Dawakin Tofa da ke da dalibai dubu 5 da 618, dukkan su na zaune a kasa.

Ya ce baya ga karancin kujeru, akwai kuma matsalolin karancin malamai da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, don haka ya yi kira ga kungiyoyin raya kasa da su tallafa wajen maganin matsalolin

Advertisement

Tun da farko, shugabar ofishin UNICEF a Najeriya, Rahama Farah, ta jaddada kudirin UNICEF na yin aiki tare da gwamnatin jihar Kano don magance matsalar yaran da ba sa zuwa maka

ranta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending