News
Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun bayyana ficewar su daga Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.
Ƙasashen uku dai su na ƙarƙashin mulkin soja ne, bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da shugabannin fararen hula a ƙasashen, inda Nijar ce ta baya-bayan nan.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito Shugabannin ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da rashin tausayin bil-Adama, biyo bayan takunkumin da aka ƙaƙaba masu.
Cikin wata sanarwar haɗin-guiwa da suka fitar, wadda aka aka watsa a gidajen talbijin na ƙasashen uku, sun ce “mun yanke shawarar tsayawa da ƙafafuwan mu, bisa doron ‘yancin mu. Don haka mun ayyana ficewar mu daga ECOWAS, saboda ƙungiyar ta kauce daga bin kyawawan manufofin da waɗanda suka kafa ta suka ɗora ta a kai, bayan shekaru kusan 50 da kafuwar ta.
“Haka kuma ECOWAS ta bi son ran wasu ƙasashen Turai, har ƙungiyar ta zama barazana ga ɗimbin al’ummar mambobin ƙasashen ta, waɗanda aka kafa ta domin ta faranta masu, ba don ta faranta wa Turawan Yamma ba.”
Ƙasashen sun fice ne bayan watannin da aka ɗauka ana kwan-gaba-kwan-baya don ganin an dawo da mulkin farar hula a ƙasashen uku.
ECOWAS ta ƙaƙaba masu takunkumi kuma har yanzu kan iyakokin Najeriya da Nijar a rufe su ke, kuma an yanke wutar lantarki daga Najeriya zuwa Nijar.
An dai shirya yin taron Ministocin Harkokin Wajen ECOWAS a Yamai, babban birnin Jamhuriyar a ranar 25 ga Janairu, amma abin bai yiwu ba.
“Tawagar ECOWAS ta yini cur a filin jirgin saman Abuja zuwa Nijar, amma daga baya aka sanar cewa “jirgin da zai ɗauke su ya samu matsala.”
