Connect with us

News

GASAR AFCON:’Ba mu ajiye Ahmed Musa a gefe hakanan kawai ba, yana mana amfani- Peseiro, kociyan Super Eagles

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

 

Kocin Super Eagles Jose Pasiero ya bayyana cewa gogaggen ɗan wasa Ahmed Musa na da amfani sosai a cikin ƙungiyar, tasu duk kuwa da cewa har yanzu bai buga wasa ko ɗaya ba a Gasar Cin Kofin Afrika.

A wasan ranar Asabar na zagaye na biyu, inda Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 2:0, an ga Lukman wanda ya ci ƙwallo ya je ya rungume Ahmed Musa da ke benci.

Kociyan Najeriya ya ce Ahmed Musa ƙwararre ne, kuma ya na bai wa ‘yan wasan Najeriya shawarwari wajen yadda za su bijiro da wani salo a yayin wasa.

Advertisement

A hirar sa da manema labarai bayan kammala wasan Najeriya da Kamaru a Corte de Ivoire, kociyan Najeriya ya ce Ahmed Musa zai buga wasa a gaba, kuma mutane su daina damuwa, domin ko a kan benci ya na yin amfani.

Masu kallo da dama a Najeriya dai sun damu ganin yadda an yi wasanni huɗu, amma Ahmed Musa bai buga ko ɗaya ba.

Musa shi ne ɗan wasan da ya fi kowa yawan buga wa Najeriya wasa, kuma ya fi kowa cin ƙwallaye tarihin kafuwar Super Eagles.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending