News
SHUGABAN KASA BOLA TINUBU YA KALLI RANTSUWAR DA USMAN ODODO DAGA KASAR FARIS
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Usman Ododo ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, bayan nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar cikin watan Nuwamba.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a Lokoja babban birnin jihar a yau Asabar da rana, inda aka rantsar da shi tare da mataimakinsa, Salifu Joel Oyibo
Sabida mahimmancin rantsuwar yasanya shugaban kasa Bola tinubu ya kalli bidiyon rantsuwar da Usman ododo daga faris babban burnin faransa
Mista Ododo wanda ɗan jam’iyyar APC ne zai maye gurbin Yahaya Bello wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na biyu. A Jigar kogin
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, da gwamnan jihar Yahaya Bello da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, na daga cikin mutanen da suka halarci bikin rantsuwar.
