News
Gwamnatin jigawa ta Kafa kotunan tafi da gidanka domin hukunta masu karya dokar tsaftar muhamlli
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya kafa kotunan tafi da gidanka guda biyar domin gurfanar da masu karya dokar tsaftar muhalli a fadin jahar
Kafa kotunan tafi-da-gidanka an yi shi ne da nufin aiwatar da dokokin muhalli da tsaftar muhalli a jihar
Duk wanda aka kama da laifin karya dokar zai fuskanci fushin doka
Kwamishinan muhalli na jihar Dr. Nura Ibrahim Dandoka ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a lokacin tsaftar muhalli na wata-wata a Dutse babban birnin jihar
Ya ce an kafa kotunan tafi da gidanka a dukkan masarautu biyar da ke jihar da suka hada da, Hadejia, Gumel, Kazaure, Ringim da Dutse.
Kafa kotunan tafi-da-gidanka an yi shi ne da nufin aiwatar da dokokin muhalli da tsaftar muhalli a jihar.
Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci ‘yan majalisar zartarwa da ‘yan majalisar jiha wajen gudanar da ayyukan tsaftar muhalli.
Ya ce manufar tsaftar muhalli na wata-wata tana da manufar inganta tsaftar mutum da muhalli a jihar.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days agoShettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
