News
Zamu Kama Duk Wanda Yake Yada Dokokin Zirga zirgar Ababen Hawa Na Karya —Hukumar KAROTA
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta karyata wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan Hukumar
Shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir ne ya karyata hakan, bayan da aka kula da rubutun yana yawo a Soshiyar Midiya wanda aka yi masa suna da “SABABBIN DOKOKIN HUKUMAR KAROTA”
Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami in yada labarai na Hukumar Nabilusi Abubakar K/Na’isa ya turawa da Jaridar Inda
Sanarwar ta kara da cewa wannan rubutu da ke kunshe a cikin Soshiyar Midiya baya cikin Sabbin Dokokin da aka sabunta a shekara ta 2022 na kundin dokar da ta kafa KAROTA a shekara ta 2012.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da kama tare da gurfanar da wadanda suke yada rubuce-rubucen karya da sunan Hukumar wajen jami’an Yansanda
Tuni Hukumar tare da jami’an tsaro suka dukufa wajen nemo waðanda suke yada jita-jitar tare da gurfanar da su a gaban sharia
A karshe Hukumar ta ce ta kusa kammala shirinta na fassara sabuwar Dokar Hukumar da aka sabunta a shekara ta 2022 wadda za a fassarata zuwa harshen Hausa domin saukakawa jama’a fahimtar abinda ke kunshe a cikin sabuwar dokar
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
