Connect with us

News

Juyin Mulkin : ECOWAS ta Yi Fatali da Shirin Mika Mulki Har Tsawon Shekaru Uku.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta ce ba za ta amince da shirin mika mulki ga gwamnatin mulkin sojan Nijar na tsawon shekaru uku ba.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Abdel-Fatau Musa ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wata hira da BBC.

Advertisement

Masu Bukata Ta Musamman Sunyi Barazanar Kai Tinubu Kotu Idan Bai Basu Kujerar Minista Ba

Shugaban mulkin sojan jamhuriya Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya bayyana a wani gidan talbijin a daren ranar Asabar cewa, sojojin za su mika mulki ga gwamnatin farar hula ne kawai nan da shekaru uku masu zuwa.

Duk da haka, Abdel-Fatau Musa, a yayin hirar, ya bayyana shawarar Tchiani a matsayin abin rufe fuska don tattaunawa da diflomasiyya.

Advertisement

Har ila yau, a ranar Asabar, tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Nijar a wani yunkuri na diflomasiyya na karshe na cimma matsaya ta lumana da gwamnatin mulkin soja.

Tawagar ta gana da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum bayan ganawa da Tchiani, amma har yanzu ba a cimma matsaya ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending