Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Damuwa Kan Yunkurin Bada Cin Hanci A Kotun Kararrakin Zabe

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwarta kan korafin da shugabar kotun sauraron kararrakin zabe ta ‘yan majalisar dokokin a Kano, Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ta ce an yi yunkurin bada cin hanci a kotun.

Idan za’a iya tunawa, Azinge ta nuna fushinta kan yunkurin wani babban Lauya mai kwarewar SAN, na ba ta cin hanci.

Advertisement

Najeriya ce kasa ta biyu da ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki—-USAID

Ko da yake, ba ta bayyana sunan babban lauyan ba.

Da yake mayar da martani kan alamarin a cikin wata sanarwa, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Baba Dantiye ya ce gwamnati ta kalli lamarin da matukar damuwa, inda ta dora laifin a kan wasu dakaru masu karfi a cikin jam’iyyar APC.

Advertisement

Ya ce dukkansu a shirye suke su yi amfani da duk wata hanya da za a bi wajen yin adalci kamar yadda aka yi a baya.

Har yanzu dai bangaren APC ba su mayar da martani kan wannan zargi ba har zuwa lokacin gabatar da rahoton a safiyar yau.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending