News
Abinda Da Zai Kawo Karshen Juyin Mulkin Sojoji A Nahiyar Afirika–Shehu Sani
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon dan majalisa kuma fitaccen mai sukar lamirin gwamnatin Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa magudin zabe ne ke haddasa rugujewar dimokuradiyya a Afirka.
Kalaman Sani na zuwa ne a daidai lokacin da aka yi juyin mulki a kasar Gabon dake Afirka ta Tsakiya.
Yadda noman rani ya zama mafita akan karancin abinci a kasar nan
Jaridar Indaranka ta rawaito cewa da sanyin safiyar yau ne jami’an soji a Gabon suka sanar da kwace mulki bayan sake zaben shugaba Ali Bongo Ondimba a karo na uku.
Rahotanni sun ruwaito cewa manyan hafsoshin sojin kasar ne suka bayyana hakan a ranar Talata a babban gidan talabijin na kasar.
An bayar da rahoton cewa, jami’an sun sanar da soke sakamakon zaben na ranar Asabar da ‘yan adawa suka yi watsi da su tare da bayyana shi a matsayin zaben shugaban kasa mai cike da magudi.
Sai dai Sani, a wani sako da ya wallafa ta dandalinshi na sada zumunta na X, ya zargi iyalan Bongo da mamayar da ruguza dimokradiyya a Gabon.
Ya rubuta cewa mutane a Gabon sun fito suna yin zanga-zanga kan tituna don nuna goyon bayan juyin mulkin da aka yi a Libreville. Iyalan Bongo sun mamaye kuma sun ruguza Dimokradiyya. Dimokuradiyya na mutuwa a Afirka muddin anayin zabe mai cike da magudi.
Kuma muddin idan har za’a cigaba da yin murdiya wajen gudanar da zabe a kasashen Afirika to ba za’a daina ganin sojoji na karbe mulki daga hannun zababbun shugabannin kasashe ba.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
