News
Dalilin Da Ya Sa A Yanzu Buhari Yake Rayuwar Nadama — Solomon Dalung
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tsohon Ministan Wasanni da Ci gaban Matasa, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa a halin yanzu tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana rayuwar nadama kan yadda makusantansa suka bata masa suna a lokacin shugabancinsa.
Dalung wanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari, ya ce gwamnatin ta gaza wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015.
Ambaliyar ruwa ta raba akalla mutane 563 da muhallansu a a jahar Adamawa
A hirarsa da gidan Radio Trust, tsohon ministan ya ce a matsayinsa na wanda suka kafa jam’iyar APC ya zama wajibi ya fadi gaskiyar abin da ke faruwa.
“Babu wani lungu da sako na kasar nan ba mu shiga a lokacin yakin neman zabe ba musamman a Arewacin Najeriya, mun dauki alkawura amma babu alkawarin da muka iya cikawa.
“Idan aka waiwaya baya, za a lura cewa babu wani abu da muka tsinana a lokacin gwamnatinmu.”
Ya ce a lokacin yakin neman zabe, sun yi wa ‘yan Najeriya alkawarin samar da tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar da kuma yakar cin hanci da rashawa, amma sai dai sun gaza cika duk alkawuran da suka dauka
Dalung ya bayyana Buhari a matsayin mutum nagari kuma shugaba mai gaskiya, wanda kuma ta aminta da mutanen da ke tare da shi, duk da cewa su ne suka bata masa suna.
“Buhari mutumin kirki ne wanda ya aminta da duk makusantansa saboda tsammaninsa duk mutanen kirki ne, amma a yanzu a dalilinsu yana rayuwa cikin nadama.
“Saboda su ne suka kai shi suka baro suka bata masa suna, sannan suka hana gwamnatinsa rawar gaban hantsi,” in ji Dalung.
Tsohon ministan ya ce gwamnatin jam’iyar APC daga tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 ta samu nasarori, domin al’amuran tsaro a lokacin ba sutabarbare kamar yanzu ba.
A wani labarin kuma Ambaliyar ruwa ta raba akalla mutane 563 da muhallansu a a jahar Adamawa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
