News
Gwamnatin Kano Ta Fara Aikin Feshin Maganin Sauro A Makarantun Kwana
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin gudanar da Feshin magungunan kwari da sauro a makarantun kwana da Tsangaya a wani mataki na yaki da kananan cututtuka tsakanin al’umma.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Alhaji Nasiru Sule Garo ne ya yi wannan alkawari lokacin da yake kaddamar da shirin Feshin magungunan kwari domin yaki da kananan cututtuka musamman cutar zazzabin cizon sauro da yake damun al’umma a wani taron da aka gudanar a sakandiren Fasaha ta GTC Ungogo dake Kano.
Gwamnatin Jahar Kano Ta Musanta Rahoton Mutuwar Mutum 10 A Rana Daya A Wani Asibitin Jihar
Nasiru Sule Garo ya ce, bayan kaddamar da aikin, gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar anyi feshin a dukkanin makarantun kwana da makarantun tsangaya.
Ya ce feshin maganin zai kawai da sauro da Beraye, Micizai da sauran Kwari da zasu iya cutar da al’umma, kuma feshin ya kamata ace ana yin sa duk shekara, inda ya bada tabbacin cewa gwamnatin ta injiniya Abba Kabir Yusuf, za ta Alaiwatar da duk wani aiki da amince domin cigaban mutanen Kano.
Kwamishinan ya ce matukar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta cigaba da rike madafun iko, gwamnatin za ta tabbatar anyi feshin maganin a kowacce shekara a don inganta lafiyar alumma.
Ya kuma bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da aikin feshin ya yi nasara.
A na sa jawabin, kwamishinan ilimi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa wanda shugaban makarantun sakandiren kimiya da fasaha na jihar Kano ya wakilta ya yabawa gwamnatin Kano bisa farfado da shirin a makarantun sikandiren wanda darakta a hukumar Alhaji Garba Ahmed ya wakilta ya bada tabbatar ma’aikatar ilimi da hukumar na ganin shirin ya samu nasara domin kula da lafiyar dalibai.
Shi kuwa, shugaban makarantar sakandiren GTC Ungogo Malam Mikail Hussain ya ce feshin ya.zo a dai-dai al lokacin da ake bukatar laakari da yadda daliban makarantar ke fama da cutar zazzabin cizon sauro a baya-bayan nan.
A wani labarin kuma Gwamnatin Jahar Kano Ta Musanta Rahoton Mutuwar Mutum 10 A Rana Daya A Wani Asibitin Jihar
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
