Connect with us

News

Duniya ta yi tur da harin Isra’ila da ya kashe mutum 500 a asibitin Gaza

Published

on

Mutane sun yi ta ɗaukar gawarwakin wadnda suka mutun daga asibitin Ah Ahli zuwa asibitin Al-Shifa hospital ranar 17 ga watan Oktoban 2023.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Isra’ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 500 a wani harin sama da ta kai kan asibiti a Gaza, inda majinyata da mutanen da suka ji raunuka da ma waɗanda ke samun mafaka sakamakon hare-haren Isra’ila duk ke ciki a lokacin, lamarin da ya jawo Allah wadai da tur da harzuƙa a Gabas ta Tsakiya da ma duniya duka.

 

Ga dai manyan martanin da wasu ƙasashe suka yi:

 

Advertisement

Falasɗinu

 

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya ce kai wa asibiti hari “mummunan kisan ƙare dangi ne na yaƙi” wanda ba za a lamunta ba, yana mai cewa babu wata tattaunawa da za a amince da ita in dai ba ta dakatar da yaƙin ba ce.

 

“Isra’ila ta ƙetare duk wasu iyakoki. … Ba za mu fice daga nan ko mu yarda wani ya kore mu ba,” ya ƙara da cewa.

 

Advertisement

Firaministan Falasɗinu Mohammad Shtayyeh ya kira harin da Isra’ila ta kai wani asibitin Gaza a mstayin “mummunan laifin yaƙi abin tsoro, kuma kisan ƙare dangi,” yana mai cewa alhakin ya kuma rataya a kan ƙasashen da ke goyon bayan Isra’ila irin su Amurka ma.

 

Turkiyya

 

“Kai hari kan asibitin da mata da yara da sauran fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ke ciki shi ne mafi kololuwar cin zali da take darajar dan’adam na hare-haren Isra’ila,” in ji Erdogan a shafinsa na X a ranar Talata.

 

Advertisement

Erdogan ya yi kira da dukkan mutanen duniya da su ɗauki matakin dakatar da “munanan hare-haren da ba a taɓa ganin irinsu ba” da Isra’ila ke kai wa Gaza.

 

“Mun damu da mutuwar ɗaruruwan Falasɗinawa da kuma ɗaruruwan da suka jikkata sakamakon harin da aka kai asibiti yau a Gaza, sannan mun yi Allah wadai da dukkan munanan hare-haren da ake kai wa da kakkasaur murya,” in ji sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

 

“Ya zama wajibi a gurfanar da duk wanda ke da hannu a kai wa fararen hula da asibitoci da makarantu hare-hare a gaban kotun ƙasa da ƙasa kan nuna rashin tausayi da jinƙai,” ta ƙara da cewa.

 

Advertisement

Pakistan

 

“Kai hari asibiti inda fararen hula ke samun mafaka da kuma kul da marasa lafiya rashin tausayi ne kuma abu ne marar dalili,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan a wata sanarwa.

 

Ta ƙara da cewa “Kai hari kan wajen da fararen hula suke da cibiyoyin lafiya mummunan take hakkin dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa ne.”

 

Advertisement

“Muna kira ga dukkan al’ummar duniya da su ɗauki matakan gaggawa na kawo ƙarshen hare-hare da ƙawanyar da Isra’ila ta yi wa Gaza da irin cin zalin da hukumominta ke yi a Gaza a ƴan kwanakin nan,” a cewar ma’aikatar.

 

Tsohon Ministan Harkokin Wajen kuma shugaban jam’iyyar masu sassauvcin ra’ayi ta Pakistan People’s Party, Bilawal Bhutto Zardari, shi ma ya yi tur da harin da aka kai asibitin, yana mai kiransa da “babbar shaida ce ta irin muguntar da Isra’ila ke yi.”

 

Saudiyya

 

Advertisement

Saudiyya ta yi Allah wadai da kakkausar murya da “mummunan laifi” na harin da dakarun Isra’ila suka kai Asibitin Al Ahly a Gaza da ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta fitar a wata sanarwa.

 

“Wannan mummunan lamarin ya tilasta wa ƙasashen duniya dole su bar munafuncin da suke yi da nuna son kai wajen fayyace dokokin hakkin ɗan’adam na duniya idan aka zo batun munanan ayyukan da Isra’ila ke aikatawa,” in ji sanarwar.

 

Kuwait

 

Advertisement

Kuwait ma ta bi sahu wajen yin tur da wannan mummunan hari da dakarun Isra’ila suka kai.

 

“Kai hari kan asibitoci ko wuraren taruwar jama’a da dakarun ƴan mamaya ke yi take dokokin duniya ne jinƙai ne,” in ji sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta fitar.

 

Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai

 

Advertisement

Shugaban Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai OIC, Hissein Taha, ya kira harin da “laifin yaƙi” da kuma “take haƙƙin ɗan’adam.”

 

Taha ya ɗora laifin a kan mamayar Isra’ila, inda ya ce tana aikata munanan hare-hare a kan Falasɗinawa, lamarin da ya ci karo da mutunta ɗan’adam da dokokin duniya na jinƙai, a sanarwar da ya fitar.

 

Masar

 

Advertisement

Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi ya ce Alkahira na sa ido sosai kan abin da ke faruwa cikin tsananin alhini.

 

“Don haka na yi Allah wadai da kakkausar murya a kan wannan hari, wanda ƙarara take dokokin duniya ne, kuma ina neman a bi tsarin dokokin mutunta ɗan’adam na duniya,” in ji Sisi a shafinsa na X.

 

Shugaban na Masar ya jaddada matsayar ƙasarsa da ta al’ummarsa a kan batun, tare da neman a yi gaggawar dakatar da hare-haren Isra’ila a Gaza da aka yi wa ƙawanya.

 

Advertisement

Qatar

 

Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta yi Allah wadai da mummunan harin bam da Isra’ila ta kai Asibitin Al Ahli Baptist a Gazar da aka yi wa ƙawanya.

 

“A kan wannan lamarin, ma’aikatar na kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki nauyin d ake kansu su hana Isra’ila sake aikata wasu laifukan a kan fararen hula,” ma’aikatar ta faɗa a wata sanarwa.

 

Advertisement

Lebanon

 

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta yi kira da “a nuna fushi na rana ɗaya a kan maƙiya.”

 

“Gobe Laraba za ta zama ranar nuna fushi a kan maƙiya,” Hezbollah ta faɗa a wata sanarwa da ta fitar.

 

Advertisement

UAE

 

Ita ma ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE Allah wadai ta yi da kakkausar murya a kan harin na Isra’ila, tana cewa tana “bayyana kaɗuwa da alhini a kan rayukan da aka rasa tare da miƙa saƙon ta’aziyyarta da jaje ga iyalai da waɗanda abin ya shafa, da kuma fatan waɗanda suka jikkata su samu sauƙi cikin gaggawa.”

 

Ta yi kira “kan yin gaggawar tsagaita wuta da tabbatar da cewa ba a kai hari kan fararen hula da wuraren taruwarsu.

 

Advertisement

Jordan

 

Sarkin Jordan Sarki Abdullah II shi ma ya yi Allah wadai da harin na Isra’ila kan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba da marasa lafiyan da ake kula da su a asibiti.

 

“Mai martaba ya ce wannan mummunan hari ne da ba za a lamunta ba, kuma dole Isra’ila ta dakatar da mugunta da cin zalin da take yi a Gaza, wanda ya yi hannun riga da dokokin darajta ɗa’adam da na jinƙai na duniya,” kamar yadda aka wallafa a shafin intanet na sarkin.

 

Advertisement

Ya yi gargaɗin cewa yaƙin ya shiga wani mataki mai muni da zai sa yankin Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya ya shiga rikici, yana maa cewa dole ƙasashen duniya su kawo ƙarshen wannan zubar da jinin.

 

TRT World

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending