Connect with us

News

Suyudi Isah  Bichi Ya Zama Sabon Shugaban Tashar Guarantee Radio Kano 

Published

on

Suyudi Isah Jibril Bichi

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Hukumar gudanarwar Gidan Radio Guarantee dake Kano, ta amice da nada Suyudi Isah Jibril Bichi amatsayin sabon shugaban tashar.

Cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Manajan gudanarwa na tashar Abdul’Aziz Habib mai kwanan wata 21-10-23, tace nadin yafara aiki nan take.

Advertisement

Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a jahar Neja

Sanarwar ta bukaci dukkanin Ma’aikata da shugabannin sassa na tashar dasu baiwa Sabon shugaban hadin kai domin dawo da martabar tashar.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Kafin wannan nadi, Suyudi Bichi shine shugaban sashin shirye shirye na gidan Radio Guarantee.

Advertisement

Suyudi Isah Jibril Bichi, yayi Diploma a fannin aikin Jarida a Kwalejin fasaha ta Jihar Kano, ya kumayi Digirinsa na farko a fannin na aikin Jarida a Jami’ar Open University, inda yake da kwarewa ta shekaru masu yawa a aikin Jarida.

Bichi ya halarci kwasa kwasai a fannoni daban daban a aikin Jarida a ciki da wajen Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending