Connect with us

News

Hukumar DSS Ta Saki Tsohon Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

An saki tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdurasheed Bawa bayan tsare shi.

Kotu Ta Aike Da Ango da Amarya da Waliyyansu Zuwa Gidan Gyaran Hali

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Bawa ne a ranar 14 ga watan Yuni, 2023, sa’o’i kadan bayan dakatar da shi daga mukamin shugabancin EFCC da shugaba Bola Tinubu ya yi masa kan zargin cin zarafi ofishin hukumar.

A daren Laraba ne aka sake shi bayan shafe watanni a tsare.

A wani labarin kuma Kotu Ta Aike Da Ango da Amarya da Waliyyansu Zuwa Gidan Gyaran Hali

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending