News
Hukumar INEC Zata Kashe Bilyan 18 Wajen Gudanar Zaben Jihohin Imo Da Kogi Da Bayelsa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Bayanan da suka fito daga cikin kudurin daftarin kwarya-kwaryar kasafin kudin bana, da majalisar zartarwa ta kasa ta amince da shi a jiya, ya nuna cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta zata samu naira milyan dubu 18 domin gudanar zaben gwamnonin jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, Atiku Bagudu, wanda ya zanta da manema Labarai na fadar shugaban kasa, kan abunda taron ya kunsa.
Majalisar Zartawa Ta Amince Da Kwarya-Kwaryar Kasafin Kudin Na Sama Da Tiriliyan 2
A wani bangaren kuma, Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fitar da bayanan yawan katinan zabe na din-din da aka karba da kuma wadanda ba’a karba ba a jihohin guda ukku.
Hukumar ta roki masu ruwa da tsaki da su kwana da sanin cewar duk inda aka samu kuri’ar da aka dangwala a rumfar zabe ta haura adadin katin zaben da aka karba a rumfar zaben, to zai kasance an samu aringinzon kuri’a.
A wani labarin kuma Majalisar Zartawa Ta Amince Da Kwarya-Kwaryar Kasafin Kudin Na Sama Da Tiriliyan 2
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
