Connect with us

News

Kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin jihar Gombe sun rufe majalisar dokokin jihar

Published

on

majalisar dokokin jihar Gombe

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya reshen jihar Gombe sun rufe majalisar dokokin jihar.

Advertisement

 An sami rahoton cewa a yau Talata kungiyar ta fada yajin aikin ne a kokarin ta na bin bayan yajin aikin da kungiyar ke yi a fadin kasar.

Lionel Messi ya sake lashe kambun gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or a karo na 8

Mambobin kungiyar ta PASAN,sun yi dafifi in da suka fito kwansu da kwarkwatan su, rike da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce iri daban-daban wadanda suka hada da cewa hakki ne na Majalisar, ba alfarma ba, tare da rera wakokin hadin kai.

Advertisement

Da yake zantawa da manema labarai a babban kofar majalisar dokokin shugaban kungiyar na jihar, Mohammed Dukku, ya ce “Wannan Matakin shi ne kadai hanya da ya da za mu bi duba da yadda gwamnatin tarayya ta kasa bin dokar da sashe na 121 (3a) na Tarayyar Najeriya ya tanadar. , wanda ya yi sharar fage akan samun ‘yancin cin gashin kan ‘yan majalisa.”

Shugaban ya kara da cewa majalisar za ta ci gaba da kasancewa a rufe kuma duka ma’aikatan majalisar za su ci gaba da zama a gida har sai Baba ta Gani.

Advertisement

Shi ma da yake nasa jawabin, sakataren kungiyar ta PASAN na jihar, Aminu Aliyu, ya kara bayyana cewa, rufe majalisar dokokin jihar ya yi daidai da umarnin da hukumar ta kasa ta bayar a kan gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da ‘yancin cin gashin kan harkokin kudi da aka baiwa majalisun.

“Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ya bayar da wannan ‘yancin cin gashin kai .Amma kuma har yanzu ba a aiwatar da tsarin ba,” ya ka

Advertisement

Har ila yau, wani daga cikin mamba a kungiyar kuma ma’aikacin Majalisar, Solomon Livinus, ya ce suna matukar goyon bayan wannan yajin aikin, “duk da cewa an fara zaman tattaunawa amma dai za su ci gaba da zama a gida,” Cewar Livinus.

A wani labarin kuma Lionel Messi ya sake lashe kambun gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or a karo na 8

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending