News
An Dage Lokacin Ganawa Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Kungiyoyin Kwadago Na Kasa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An dage ganawar da aka shirya yi tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya, dangane da alkawarin da bangarorin biyu suka kulla na biyawa kungiyoyin kwadago bukatunsu kafin cikar wa’adin kwanaki 30.
Wani babban jami’in kungiyar kwadago, wanda ya zanta da jaridar PUNCH, ya ce a halin yanzu za’a yi ganawar nea Talatar makon gobe.
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Kama Wadda Ake Zargi Da Kisan Malamar Jami’a A Minna
Jami’in wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce an dage ganawar ne kasancewar, ranar litinin da aka tsara yin taron ita ce lokacin da ake gudanar da zaman majalisar zartawa na kasa.
Ya sake jaddada matsayarsu na daukar matakin da ya dace da zarar wa’adin da suka bayar yak are muddin ba biya masu bukatunsu ba.
A wani labarin kuma Rundunar ‘Yan Sanda Sun Kama Wadda Ake Zargi Da Kisan Malamar Jami’a A Minna
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
