Connect with us

News

Sanata Natasha Ta Zargi Gwamnan Jahar Kogi Da Yunkurin Halaka Ta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Zababbiyar sanatar kogi ta tsakiya da kotun daukaka kara ta tabbatar da nasararta a jiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, ta zargi gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da hada makarkashiyar cutar da ita a yayin zaben sanatoci da aka yi cikin watan Maris din bana.

Ta yi wannan zargin ne a ranar Talata ta cikin shirin Siyasa a yau, na gidan Talabijin na channels, Ta ce ta jiwo karar harbin bindiga akan motar da take ciki, kuma da bidiyo a matsayin hujjar da zata tabbatar da zargin nata.

Advertisement

Bayanai kan sayen ‘jirgin ruwan kasaita na Shugaban Kasa’ a kasafin Kasa na 2023

Ta yi zargin cewar mutanen da suka rika harbin motar tata suna sanye ne da riga mai dauke da tambarin jam’iyyar APC , Kuma daya daga cikinsu shine baturen zabe na karamar hukumar Okehi.

 

Advertisement

Haka zalika sanata Natasha Akpoti ta yi zargin cewar da gangan gwamnan jihar ya lalata wasu hanyoyi dake cikin jihar, domin kawo tazgaro wajen gudanar da zaben.

A wani labarin kuma Bayanai kan sayen ‘jirgin ruwan kasaita na Shugaban Kasa’ a kasafin Kasa na 2023

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending