News
Gwamanatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 15 Domin Gyaran Gadar Jahar Legas
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 15 domin gyaran gadar nan ta Third Mainland dake Legas, kamar yadda bayanai suka nuna daga karin kasafin kudi na naira tiriliyan 2.18 na shekarar 2023.
Haka kuma, gwamnatin ta bayyana cewa tana bin ‘yan kwangilar gadar Eko/Marine bashin Naira biliyan 11.4.
Kotun daukaka kara ta sanya ranar sauraren karar zaben Gwamnan Kano
Kwanturolan ayyuka na gwamnatin tarayya a jihar Legas Olukorede Kesha, a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa za a rufe gadar ta Third Mainland na tsawon makonni biyar na gyaran gadar da za a fara daga ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023.
Bisa abubuwan da ke sama, yanzu ana sanar da jama’a masu ababen hawa cewa za a fara aikin gyarawa tare da ramukan da ke haɗa Oworoshoki zuwa Adekunle da Legas-Island (Adeniji Adele) zuwa Adekunle a lokaci guda.
Daily Post ta rawaito cewa Saboda haka, hanyoyin biyu da aka ambata a sama za a rufe su don zirga-zirga da karfe 7 na safe ranar Litinin, Nuwamba 6, 2023, na tsawon makonni biyar.
A halin da ake ciki, yayin karin kasafin kudin na ma’aikatar ayyuka, Ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya koka da yadda ake ci gaba da durkushewar gadoji a fadin kasar nan.
A wani labarin kuma Kotun daukaka kara ta sanya ranar sauraren karar zaben Gwamnan Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
