News
Kare dan alkawari da ya shafe mako 10 cikin daji a kusa da gawar mai shi
Wani kare da aka samu a raye a gefen gawar mai ita makonni 10 bayan sun ɓace a tsaunin Colorado ta rayu ne ta hanyar farautar ƙananan dabbobi, in ji masu ceto.
Rich Moore, mai shekaru 71, tare da Jack Russell terrier, Finney, sun yi niyyar hawan tsaunin Blackhead a ranar 19 ga watan Agusta, amma ba su dawo gida ba.
An gano gawar Mr Moore a ranar 30 ga watan Oktoba, tare da Finney a gefensa. Masu ceto sun ce tsira da karen ya yi “kyakkyawan labari ne”.
Delinda VanneBrightyn, na ƙungiyar sa kai ta Taos masu aikin ceto, ta ce masu aikin ceto sun yi wani bincike na tsawon kwanaki da bai yi nasara ba a gaɓar yammacin tsaunin da ke tsakanin inda motar Mista Moore ke ajiye.
Makonni bayan haka wani mafarauci ya gano gawar Mista Moore a cikin tsaunin San Juan – kimanin kilomitoci 2.5 gabas da kololuwar – tare da Finney wanda ke raye.
An tura jami’an ceto zuwa tsaunin washegari. An kai karen zuwa wurin likitan dabbobi kuma yanzu yana tare da dangin Mista Moore.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
