News
An Kai Hari Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Adamawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari kan hedikwatar ’yan sanda da ke Jihar Adamawa.
Rugugin luguden harbe-harben maharan a cikin dare ya jefa mazauna garin Jimeta da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa a jihar cikin tashin hankali.
Ronado Da Messi Za Su Hadu A Wani Wasan Sada Zumunci A Watan Fabrairu
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya cewa hedikwatar rundunar ce aka kai wa hari, kuma ba a kai ga gano maharan ko manufarsu ba.
Sai dai ya bayyana cewa jami’an rundunar sun yi nasarar fatattakar maharan, bayan musayar wuta ta kusan minti 30 da misalin karfe 11 na daren Talata.
Wasu majiyoyi dai sun yi zargin maharan sojoji ne suka kai harin daukar fansa kan hedikwatar rundunar kan kisan wani hafsan soja da wani dan sanda ya yi.
Kawo yanzu dai ana bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
