Connect with us

News

An Tsaurara Tsaro Yayin Da Ake Shirin Yanke Hukunci Akan Zaben  Nasarawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

An saka tsauraran matakan tsaro a harabar kotun daukaka kara da ke Abuja yayin da kotun za ta yanke hukunci a shari’ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Jami’an tsaro dauke da makamai daga rundunar ‘yan sandan Najeriya, da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da kuma jami’an tsaron farin kaya sun killace dukkanin hanyoyin da ke zuwa kotun daukaka kara.

Advertisement

Majalisa Ta Fara Bincike Akan Naira Tiriliyan 12 Da Aka Kashen Wajen Gyaran Matatun Mai

Motoci masu zaman kansu da na ‘yan kasuwa da ke bin hanyoyin sakatariyar gwamnatin tarayya zuwa wurare daban-daban, an karkatar da su zuwa wasu hanyoyin tare da jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, inda suka yi ta gwabzawa domin shawo kan cunkoson ababen hawa da suka samu kan hanyar.

Mahukuntan kotun ne suka aiwatar da matakan tsaron, kamar yadda jaridar DAILY POST ta tattaro, domin dakile yiwuwar karya doka bayan yanke hukunci.

Advertisement

Har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto, duka ma’aikatan kotun, lauyoyi, masu kara da kuma manema labarai suna ta kutsawa cikin babbar kofar shiga harabar kotun.

Duk da cewa an amince da wasu ‘yan jarida da dama da suka bayar da labarin yadda aka yanke hukuncin, biyar daga cikinsu ne kawai aka ba su damar shiga cikin dakin kotun saboda abin da wani jami’in kotun ya dorawa laifin rashin isasshen kujeru da kuma kula da jama’a.

Advertisement

Wakilinmu ya lura da cewa wasu daga cikin jami’an jam’iyyar siyasa da aka amince da su da masu goyon bayansu da suka isa kotun tun da karfe 8 na safe ne aka ba su izinin shiga harabar kotun, yayin da wasu da dama kuma ‘yan sandan tafi da gidanka dauke da makamai suka hana su zuwa nesa.

Za a yanke hukuncin tsakanin gwamna mai ci a jihar Abdullahi Sule na jam’iyyar APC da abokin hamayyarsa David Ombugadu na jam’iyyar PDP.

Advertisement

A wani labarin kuma Majalisa Ta Fara Bincike Akan Naira Tiriliyan 12 Da Aka Kashen Wajen Gyaran Matatun Mai

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending