News
Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa gwamna Abdullahi Sule nasara
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a Abuja ta tabbatar da nasarar zaɓen gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Kotun ta kuma yi watsi da hukuncin da kotun sauraron korafin zaɓe ta yanke a ranar 2 ga watan Oktoba, inda ta kori Abdullahi Sule na jam’iyyar APC tare da ayyana David Ombugadu, ɗan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar.
An Tsaurara Tsaro Yayin Da Ake Shirin Yanke Hukunci Akan Zaben Nasarawa
Da suke yanke hukunci, alkalan kotun guda uku, sun ce kotun korafin zaɓe tayi kuskuren yanke hukuncin cewa Sule bai samu yawan kuri’un da aka kaɗa a zaɓen ba.
Advertisements
