News
Mutum 25,000 ne suka ɓace a cikin shekaru 10 a Najeriya – ICRC
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa Red Cross a Najeriya ta ce ƙasar ta samu mutum sama da 25,000 da suka ɓata cikin shekaru 10 da suka gabata.
Da yake zantawa da manema labarai, jami’in hulɗa da jama’a na ICRC a Najeriya Aliyu Dawobe, ya bayyana an samu adadin ne bayan da ƴan uwan mutane suka zo suka shigar da batun a wurin ƙungiyar ta Red Cross.
Dawobe ya ce, “ICRC ta fara haɗa kan iyalai ne a shekarar 2013 a Najeriya.
Ya ce mutum 25,000 da suka ɓace kaɗan ne daga cikin mutanen da suka san cewa ICRC na taimakawa wajen haɗa ’yan uwa da suka rabu da iyalansu.
Dawobe ya ce sun yin rajistar korafe-korafensu kuma akwai fiye da batutuwa 25,000 da aka shigar gaban ICRC.
Sai dai jami’in na ICRC ya ce alkaluman mutanen da suka ɓata a Najeriya a cikin shekaru goma da suka wuce za su iya raguwa sakamakon cewa wasu iyalai na sake haɗuwa da ƴan uwansu ba tare da taimakon ƙungiyar Red Cross.
A wani labarin kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa gwamna Abdullahi Sule nasara
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
