Connect with us

News

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya biya kudin aikin da za a yiwa matashinnan Abdurraba

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya biya kudin aikin da za a yiwa matashinnan Abdurraba dan karamar hukumar Kunchi da ya samu lalura wanda fuskarsa ta kunbura.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Shugaban ma’aikatan Ofishin Sanata Barau Farfesa Muhammad Bin Abdallah ne ya jagoranci biyan kudin aikin Naira Miliyan daya ga matashin a wannan Rana ta Alhamis 23 ga Nuwambar 2023.

Advertisement

Shugaban mulkin sojin Nijar ya kai ziyararsa ta farko ƙasar waje

Muhammad Bin Abdallah ya ce Sanata Barau ya fiya kudinne sakamakon yadda matshin ke tsananin bukatar kulawa, baya ga yadda matashin ke kokarin neman na kansa.

Matashi Abdurraba dai ya gamu da wani ciwo da kawo yanzu haka fuskarsa ta kunbura kuma ciwo na damunsa, da ta kai baya iya komi yana zaune a gida.

Advertisement

Amma dai likitoci a Asibitin Malam Aminu Kano sunce, ba za a yiwa matashin aikin ba, sai zuwa fuskarsa ta sace.

Tuni ake ci gaba da mika sakon jaje da kuma mika sakon alhinin abin da ya faru ga matashin wanda a baya dalibi ne da ya kammala jama’ia.

Advertisement

Itama Mahaifiyar matashi Abdurraba ta bayyana farin cikin wannan tallafin kudin da aka biya dan nata, duk da cewa dama suna cikin wani hali.

Ta kuma sake nuna farin cikinta ga duk wanda suka tallafawa dan nata bisa wannan hali da ya tsinci kansa a ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending