Connect with us

News

Simon Lalong ya karbi takardar shaidar cin zaben Sanata

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Tsohon gwamnan Filato, Mista Simon Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe ta kasa INEC a yau Alhamis.

Matakin ya zo ne, bayan kotun daukaka kara a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da nasarar da ministan kwadagon na Najeriya ya samu a karamar kotu, inda ta yi watsi da karar da abokin takararsa Napoleon Bali ya daukaka.

Advertisement

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya biya kudin aikin da za a yiwa matashinnan Abdurraba

Karamar kotun ta soke zaben Napoleon Bali bisa hujjar cewa jam’iyyarsa ta PDP ba ta da halastaccen shugabanci a lokacin da ta tsayar da shi takara.

Sai dai, babu masaniya karara ko hakan na nufin Simon Lalong, zai ajiye mukaminsa na ministan kwadago wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada shi, watanni bayan kammala zaben watan Fabrairu, don wakiltar jama’ar Filato ta Kudu a majalisar dattijan Najeriya.

Advertisement

A wani labarin kuma Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya biya kudin aikin da za a yiwa matashinnan Abdurraba

Gwamnan Kogi Yahaya Bello Ya Rufe Asusun Gwamnatin Jihar

Advertisement

Yanzu haka dai gwamnatin Kogi ta bayar da umarnin garkame dukkan asusun Gwamnatin jihar da na kananan hukumomi ba tare da wani bata lokaci ba.

Sanarwar da Kwamishinan Kudi, Asiwaju Asiru Idris ya sanya wa hannu, ta ce babu wani zargi ko wani nau’i na biyan kudi daga asusun gwamnatin jihar daga yanzu.

Advertisement

A cewar sanarwar, “An soke duk wani umarni na tsaye da kuma umarnin saka hannun jari nan da nan.

“An kulle dukkan asusun jihar Kogi daga yau Alhamis 22 ga watan Nuwamba 2003.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending