News
Kotun Koli za ta yi adalci ga Mutfwang, da kuma Lawal – Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi imanin cewa kotun koli za ta yi adalci kan korar Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da takwaransa na Jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal da kotun daukaka kara ta yi.
Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi a Abuja ranar Alhamis sun bayyana da cewa Hakan kamar “ koma baya na wucin gadi” hukuncin biyu da kotun daukaka kara ta yanke na korar mambobinsu biyu a makon jiya.
Taron na ranar Alhamis ya gudana ne a gidan Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a Abuja inda wasu gwamnoni shida suka halarta tare da wasu da mataimakansu suka wakilce su.
A cikin sanarwar da suka fitar a karshen tattaunawarsu, gwamnonin ‘yan adawar sun ce, “Taron ya yi nazari kan hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ta yanke a baya-bayan nan game da gwamnonin Jihohi daban-daban, kuma an yi la’akari da sakamakon daban-daban.
“Mun yi imanin cewa Kotun Koli za ta yi adalci a shari’ar da muka samu na wucin gadi kamar jihohin Zamfara da Filato.”
Game da zabukan da aka yi a jihohin Kogi, Bayelsa, da Imo, gwamnonin PDP “sun goyi bayan matakin da INEC ta dauka na binciki zargin da ake yi na cewa akwai takardun cike da kura-kurai tun kafin a fara zabe a wasu wuraren domin tabbatar da kwarin gwiwar jama’a. a tsarin zabe”.
A makon da ya gabata, kotun daukaka kara ta kori gwamnoni uku da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana a matsayin wadanda suka yi nasara a zaben watan Maris na 2023. Dukkan gwamnonin ukun da kotun daukaka kara ta kora suna jam’iyyun adawa ne, lamarin da ya kara haifar da fargabar cewa jam’iyyar APC mai mulki na amfani da bangaren shari’a wajen yakar jam’iyyun adawa amma APC ta musanta wannan zargi.
Kotun ta kori gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) tare da bayyana takwaransa na jam’iyyar APC, Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
