Uncategorized
Kowa Na Da Irin Gudummuwa Da Zai Bayar Dan Hana Mace Macen Mata Masu Ciki — Dakta Habib Sadauki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar likitoci masu kulada Mata na kasa sun gudanar da taron shekara na kasa a jihar Kano.
Taron na bana mai taken “Mace macen Mata hakkine da ya rataya akan kowa wajen bada gudummuwa domin kariya”.
Da yake bayani ga yan jarida akan taron shugaban qungiyar na kasa Dakta Habib Sadauki ya ce taron na shekara-shekara an kawo shi jihar Kano ne bana dan tattauna matsalolinda ke addabar Mata musamman wajen haihuwa dan a sami mafita.
Aisha Bura Ta Zama Shugabar Kungiyar Mata ‘Yan Jarida Ta Najeriya
Ya ce kowa na da irin gudummuwa da zai bayar dan hana Mace macen na farko ita kanta Matar in ta sami ciki ta je Asibiti tayi awon ciki in lokacin haihuwa ya yi aje Asibiti a haihu.
Ya yi nuni da cewa magida da yan’uwa da makota sunada gudummuwa da zasu bada dan a taimakawa mace ta yi renon ciki har ta samu ta haihu lafiya lau Rashin haihuwa a Asibiti yana zuwa da matsaloli da yawa musamman idan aka bari sai abubuwa sun ta’azzara kafin a tafi Asibi.
Ya koka da cewa sai abar mace a gida ta soma naquda sai tace zata iya haihuwa a gida sai jini ya valle Mata kafin taje Asibiti sai a samu abubuwa su taso masu yawa shi yasa akeso kowace Mata idan haihuwa tazo aje Asibiti.
Ya ce Gwamnati tanada hakki ta tabbatar cewa Asibitoci suna da kayan aiki na zamani da ruwa da wuta da kayan aiki da ma’aikata wadanda zasu kulada matan in sun zo haihuwa.
Dakta Habib Sadauki yace mafita da za’a cimma na ka’ida da majalisar dinkin Duniya ta tanada na kulada Mata a kasarnan shine yanda ake ta samarda jami’oi a kasarnan dan horar da samar da ma’aikatan lafiya.
Ya ce akwai wasu jami’an lafiya da ake horar dasu suna bada kulawa ga Mata masu juna biyu in abu ya baci ya gagaresu ne sai a kaiwa likita domin tun daga Matakin lafiya na farko ake somawa zuwa babban Asibiti har aje ga Asibitin kwararru duk ba sai lallai ansa likita a wajen ba, in aka sami ma’aikatan lafiya masu ilimin kulada Mata da taimaka musu in sun zo haihuwa za’a rage matsalar .
Dakta Habib Sadauki ya ce sunada kyakkyawan danganta da masu karvar haihuwa na gargajiya amma suna basu shawara su riqa kai Mata da suka ga suna dogon naquda Asibiti ba sai ta baci ba shine babban aikinda yakamata suyi.
Dakta Habib Sadauki shugaban qungiyar likitoci masu kulada harkokin Mata na Nijeriya na yi Kira ga Gwamnatin tarayya dana jihohi su tabbatar cewa sun baiwa Mata dama na haihuwa a Asibitoci kyauta su je Asibiti ma’aikata su kula dasu da basu magani kyauta kar ace sai sun kawo kudi wannan yana kawo jinkiri wajen samun lafiya kuma kmar Gwamnatin jihar Kano ta dade tana taimakawa idan za’a haihu kyauta Kuma har yanzu ana kamantawa.
