News
Majalisar Dokokin Ondo Na Shirin Aiyana Mataimakin Gwamnan Jihar A Matsayin Mukaddashin Gwamna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Bayan wata ganawar sulhu da shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi da jagororin jihar Ondo a ranar Juma’ar data gabata, A halin yanzu ‘yan Majalisar dokokin jihar zasu gana a yau domin tattauna yanayin siyasar da jihar ke ciki.
Wata majiya daga zauren majalisar dokokin jihar ta fadawa jaridar Punch cewar, Daya daga cikin manyan abubuwan da ‘yan majalisar zasu tattauna shi ne, Yiyuwar aiyana mataimakin gwamnan jihar Lucky Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamnan jihar, biyo bayan dogon lokacin da aka dauka batare da ganin fuskar gwamnan a jihar ba.
Ƴan Najeriya sun kashe N2.6tn wajen sayen katin waya da data a cikin watanni 9
A lokacin da aka tuntubi kakakin majalisar Olamide Oladije domin jin ta bakinsa, Ya ce yana cikin taro ne, kuma kawo yanzu da muke baku labarin babu wata amsa da ya bayar.
Majalisar dai ta jingine kudirinta na tsige mataimakin gwamnan jihar daga kan kujerarsa tun bayan ganawar da suka yi da shugaban Kasa Bola Tinubu.
A wani labarin kuma Ƴan Najeriya sun kashe N2.6tn wajen sayen katin waya da data a cikin watanni 9
An shiga rana ta biyar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, bayan Qatar da ke shiga tsakani ta sanar da tsawaita wa’adin da sa’o’i 48, domin samun damar musayar ƙarin fursunoni tsakanin bangarorin biyu.
Ofishin Firaiministan Isra’ila ya ce an ba su sunayen Isra’ilawa 10 da Hamas za ta saka a yau Talata, wanda ta yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.
Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya yi maraba da wannan labari inda ya ce yana fatan wannan tsagaita wuta zai sanya mutane su koma cikin hankalinsu, da fahimtar tashin hankali da amfani da karfin soji ba za su magance matsalar ba.
Ita ma Isra’ila ta bada sunayaen Falasdinawa mata 50 da ka iya samun ‘yanci kafin karewar wa’adin a ranar Alhamis.
