News
Kotu ta bukaci Abba ya biya Alhassan Ado Doguwa diyyar miliyan 25
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a birnin tarayya Abuja ta bukaci gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, da ya biya dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun-wada Alhassan Ado Doguwa diyyar naira miliyan 25 sakamakon bata masa suna da kuma razana shi kan zargin cewa shine wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu ‘yan jam’iyyar NNPP a garin Tudunwada yayin babban zaben kasa da ya gudana.
Tun farko dai Alhassan Ado Doguwa ne ya garzaya gaban kotun inda ya yi zargin cewa, gwamnan na Kano yana shirya masa wata makarkashiya a karkashin kasa da ya ke son jami’an tsaro su kama shi idan ya zo Kano kan zargin kisan mabiya jam’iyyar NNPP a garin na Tudunwada duk kuwa da cewa gwamnatin Kano da ta gabata ta wanke shi kan wannan zargi.
Babbar kotun jihar Jigawa ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu mazaje biyu
Mai shari’a Nnamdi Dimgba na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ja kunnen gwamnatin jihar Kano da duk wata hukuma da ta guji kama Alhassan Ado Doguwa kan wannan batu.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa a yayin babban zaben kasa da ya gudana, an kona ofishin jam’iyyar NNPP a garin Tudunwada wanda sanadiyar haka wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka rasa rayukansu, wanda kuma jam’iyyar NNPP ta zargi shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan na Nigeria a waccan lokaci da daukar nauyin wadanda suka aikata wannan ta’addanci.
Wannan lamari dai ya kai har ‘yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, suka gurfanar da shi gaban kotu kafin daga bisani kotu ta bada belinsa kan kudi naira miliyan 500.
Daga bisani dai bayan wasu kwarya-kwaryar bincike gwamnatin jihar Kano ta waccan lokaci ta wanke Alhassan Ado Doguwa kan wannan zargi, wanda ta ce, babu wani cikakken hujja da za a dogara dashi a alakanta shi kan wannan lamari.
