Connect with us

News

CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Babban bankin kasa (CBN), ya sanar da matakin haramta hada-hadar kudi a asusun ajiyar banki da babu BVN da lambar NIN daga watan Maris din 2024.

A wata takardar da aka raba wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kudi da masu gudanar da hada-hadar kudi, CBN ya ce za a hana amfani da asusun ajiyar.

Advertisement

Kotu ta bukaci Abba ya biya Alhassan Ado Doguwa diyyar miliyan 25

Babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne asusu ya zamana yana da BVN ko NIN.

Leadership ta ruwaito cewa CBN ya ce nan ba da dadewa ba za a gudanar da cikakken bincike kan asusun da babu BVN ko NIN, kuma da zarar an samu babu za a dakatar da asusun.

Advertisement

“Dukkan cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke jagoranta ana bukatar su yi aiki da tsauraran matakai kan takunkumi kan asusun ajiya,” in ji Efobi da Mustapha a cikin takardar sanarwar

A wani labarin kuma Kotu ta bukaci Abba ya biya Alhassan Ado Doguwa diyyar miliyan 25

Advertisement

Ƙungiyar Mayaƙan Hezbollah da ke Lebanon ta harba makamai kan dakarun Isra’ila da ke kan iyakar ƙasar, bayan da Isra’ila ta koma kai hare-hare a Gaza.

Sojojin na ISra’ila sun ce sun mayar da martani, inda suka ce sun harbo wani jirgi marar matuƙi da suka ce an turo shi daga Lebanon.

Advertisement

Hezbollah, wadda ke samun goyon bayan Iran – ta ce an kashe mutum biyu a garin Houla da ke kan iyakar kudancin ƙasar.

Kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kusan mutum 100 – mafi yawansu mayaƙan Lebanon – aka kashe lokacin da ake tsaka da musayar wuta tsakanin Hezbollah da dakarun Isra’ila a kan iyakar.

Advertisement

Ita ma Hamas ta harba makaman roka zuwa cikin Isra’ila, inda aka riƙa jin ƙarar na’urar ankararwa a garuruwan da ke tsakiyar Isra’ila.

Sai dai dakarun na Isra’ila sun ce babu ɗaya daga cikin rokokin da ya faɗa a birnin Tel Aviv, sannan kuma babu rahoton jikkata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending