Connect with us

News

Sanatocin Nijeriya 109 Sun Yafe Albashinsu Na Watan Disamba Domin Tallafawa Mutanen Tudun Biri

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Sanatoci 109 na Tarayyar Najeriya sun bayar da gudunmawar albashin watan Disamba ga wadanda harin bam da ya rutsa da su a Kaduna a ranar Lahadi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne ya sanar da hakan a ranar Lahadin da ta gabata a gidan gwamnatin Jihar Kaduna a lokacin da ya jagoranci wata babbar tawaga ta ‘yan majalisar dattijai zuwa jihar.

Jirgin sojin Sama  ya halaka gomman ‘yan ta’adda da baburansu 18 a cikin jirgin ruwa

Barau ya bayyana cewar saboda matukar nuna alhini da sanatocin Nijeriya suka yi sun dauki matakin yafe dukkan albashinsu na watan Disamba,domin a tallafawa mutanen da harin bam na Tudun Biri ya rutsa dasu.

 

Advertisement

Gwamna Uba Sani ne ya tarbi Sanatocin a gidan gwamnatin jahar Kaduna an Sir Kashim House dake birnin Kaduna,inda ya nuna matukar godiyar gwamnatin jahar akan nuna kulawa da sanatocin suka yi ga wadanda harin jirgin Tudun Biri ya rutsa dasu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending