News
Gwamatin Jihar Kano Za Ta Sake Bude Sabon Asibitin Masu Tabin Hankali.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da sake bude sabon asibitin masu tabin hankali a Cibiyar Kula da Masu Larurar Kwakwalwa da ke Dorayi Babba.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan asibitin masu tabin hankali na gwamnatin tarayya, wanda a baya shi ne asibitin masu tabin hankali na Dawanau a dakin taro na Hukumar Kula da Manyan Asibitoci.
Sanatocin Nijeriya 109 Sun Yafe Albashinsu Na Watan Disamba Domin Tallafawa Mutanen Tudun Biri
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Ya ce daukar matakin ya zama dole domin magance matsaloli da kalubalen da majinyata ke fuskanta, ya kuma ce rahotanni na nuna cewa majiyyata kan shafe kusan kwana guda ba tare da sun ga likita ba.
Kwamishinan ya bayyana cewa bisa la’akari da haka, tare da cewa har yanzu ma’aikatan asibitin na nan a cikin tsarin biyan albashin gwamnatin jihar Kano bayan watanni bakwai da gwamnatin tarayya ta karbi asibitin, Alhaji Abba Kabir Yusuf bai gamsu da wannan al’amari ba, wanda ke shafar ma’aikata da marasa lafiya da ke ziyartar asibitin don samun kulawar likita.
Dakta Labaran, wanda ya samu wakilcin Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Manyan Asibitoci, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya bayyana cewa tuni mai girma Gwamna ya umarci ma’aikatar ayyuka da ta fara inganta ayyukan daga likkafar cibiyar kula da masu larurar kwakwalwa ta Dorayi domin tabbatar da gyara gine-ginenta da kuma samar da dukkan kayan aikin da ake buƙata.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, an umurci hukumar kula da manyan asibitoci da ta dawo tare da sake tura dukkan ma’aikata 105 da ke aiki a asibitin masu tabin hankalin zuwa sabon asibitin da aka sake budewa su kuma fara gudanar da aiki ba tare da bata lokaci, yana mai jaddada cewa dole ne dukkan ma’aikatan su zo bakin aiki ranar Litinin.
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin halinsa na tausayi ba zai bari a jefa rayuwar al’ummarsa cikin garari ta kowace hanya ba, yana mai jaddada cewa Gwamnan, a matsayinsa na mai tafiyar da gwamnati daidai da bukatun jama’a, ya kuduri aniyar yin duk mai yiwuwa wajen samar da yanayi mai kyau na kula da al’ummar jihar.
Kwamishinan ya kuma yaba wa Gwamnan bisa bayar da gudummawa ta musamman ga bangaren lafiya na jihar wanda ya shaida samun sauyin da ba a taba samu ba a cikin kankanin lokaci.
Daga nan sai ya bukaci ma’aikatan da su yi tsayuwar daka wajen ganin sun biya bukatun majinyata domin ma’aikatar da hukumar HMB ba za su lamunci lalaci da sakaci da aiki daga kowane ma’aikaci ba.
