News
Hukumar EFFC na bukatar majalisa tayi doka a kan masu zama attajirai dare guda
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Sabon shugaban hukumar EFCC dake yaki da cin hanci da rashawa , Ola Olukayode ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta samar da wata dokar da zata bai wa hukumarsa damar gudanar da bincike a kan mutanen dake yin arziki dare guda ba tare da sanin sana’ar da suke yi ba.
Olukayode yace idan majalisa tayi sabuwar dokar, zata taimaka musu wajen hukunta masu satar dukiyar jama’a da kuma zama attajirai dare daya.
Gwamnan Jihar Kano Da Gwamnoni 12 Na Fuskantar Rashin Tabbas A Hukuncin Kotun Ƙoli
Shugaban hukumar yace tuni wasu kasashe irinsu Birtaniya da Australia da Mauritius da Kenya da kuma Zimbabwe suka amince da irin wannan doka, wadda ta basu damar gudanar da bincike domin gano yadda irin wadannan attajirai suka tara dukiya ba tare da sanin kasuwancin da suke yi ba.
Olukayode yace wannan matsalar ba wai ta tsaya a Najeriya bane, ganin yadda kasashe da dama ke sabunta dokokin su domin tafiya da zamani da kuma dakile yadda ake halarta kudaden haramun.
Shugaban hukumar yace samar da irin wannan doka a Najeriya zai bai wa jami’an hukumarsa damar tinkarar irin wadannan attajiran dare daya da kuma gano inda suka samun dukiyarsu.
FRI Hausa ta ruwaito cewa EFCC tace rashin samar da dokar da ake bukata, zai dakile kokarinsu na shawo kan matsalar cin hanci da rashawa wanda ke yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.
Hukumar EFCC ta samu gagarumar nasara wajen kwato kadarorin da barayin gwamnati suka mallaka ba bisa ka’ida ba da kuma nasarar daure da dama daga cikinsu.
Irin wadannan kadarori sun hada da gidaje da motoci da jiragen ruwa da kuma filaye.
Cikin wadanda tayi nasarar daurewa harda tsoffin gwamnoni da ‘yan majalisu da kuma ministoci.
A wani labarin kuma Gwamnan Jihar Kano Da Gwamnoni 12 Na Fuskantar Rashin Tabbas A Hukuncin Kotun Ƙoli.
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
