Connect with us

News

Jawabin Shugaba Tchiani yayin da Nijar ta cika shekara 65 da zama jamhuriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

A yau Litinin ne ƙasar Nijar ke cika shekara 65 da zama jamhuriya sai dai lamarin na zuwa ne daidai lokacin da ƙasar ke cikin wani yanayi sakamakon takunkuman da aka ƙaƙaba mata bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Shugaban mulkin sojan kasar Janar Abdourahamane Tchiani a jawabin da ya yi wa ƴan ƙasar ya taɓo batutuwa da dama da suka shafi damina da tsaro da cin hanci da rashawa da siyasa da kuma rashin shugabanci na gari.

Kotu ta Daure wasu Matasa a Jahar Kano saboda Laifin Buga Ludo da Shaye-Shaye a Masallaci.

Janar Tchiani ya ce “ta dalilin nasarorin da dakarun ƙasar ke samu a fage daban-daban, kwanciyar hankali ta fara dawowa inda ake samun raguwar hali na rashin tsaro a ƙasar,”

Ya ce an samu komawar ƴan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali, an kuma buɗe makarantu kusan 200 bayan shafe sama da shekara biyu a rufe saboda matsalar rashin tsaro a Tillaberi.

A cewarsa an samu ci gaba ta ɓangaren samar da tsaro ga ayarin da ke samar da abinci da magunguna da kuma farfaɗowar ayyukan yau da kullum ga al’ummomi a wasu jihohin ƙasar.

Advertisement

Ya kuma jinjina wa jami’an tsaron ƙasar da suka bayar da gudumawa wajen nasarorin da aka samu ta dalilin jajircewarsu.

Takunkuman Ecowas

Game da takun-saƙa tsakanin sojojin Nijar da ƙungiyar Ecowas kuwa, Janar Tchiani ya bayyana matakin da aka ɗauka a kan ƙasar da “rashin hankali da rashin imani da ta’addanci.”

Shugaban ya kuma yaba wa gwamnatocin Guinea da Chadi da Algeria da Equitorial Guinea da Morocco da Togo da sauran ƙasashen ƙawance da suka ba su goyon baya a lokutan da ya kira “masu wahala”.

Bbc ta ruwaito cewa Janar Tchiani ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Kungiyar Ceton jamhuriyar Nijar ne bayan kwace iko a ranar 26 ga watan Yuli.

Har yanzu sojojin da suka kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin na Nijar na ci gaba da tsare Mohammed Bazoum da wasu daga cikin iyalansa.

Advertisement

Duk wani yunƙuri na sulhuntawa tsakanin sojoji masu juyin mulkin da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Ecowas/Cedeao ya ci tura.

An ƙaƙaba takunkumai a kan ƙasar, lamarin da ya haifar da taɓarɓarewar al’amura da wahalhalu ga al’ummar ƙasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending