Connect with us

News

Kotun Koli ta Sanya Ranar sauraren karar Zaben Gwamnan Jihar Kano  

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Kotun koli ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamba domin sauraren karar zaben gwamnan Kano.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka aikewa bangarorin biyu daga kotun ƙolin.

AIA Kurawa TRAVELS AND GENERAL CONTRACTS LTD ya gabatar da Shafin Yanar gizo

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 17 ga watan Nuwamba, kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke, wadda ta kori Gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Dr Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kwamitin mutum uku na kotun daukaka kara ya yi watsi da karar da Gwamna Yusuf ya shigar bisa la’akari da matsayinsa na mamba a jam’iyyarsa. Sai dai rudani ya faru a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba lokacin da aka fitar da daftarin hukuncin.

Advertisement

Wannan dai Shari’a dake gaban kotun ƙoli kan zaɓen gwamnan jihar kano ita ce zata kawo ƙarshen takaddamar da ake tsakanin jam’iyyar APC

da NNPP.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending