News
Kotu ta Daure wasu Matasa a Jahar Kano saboda Laifin Buga Ludo da Shaye-Shaye a Masallaci.
DAGA BASHIR AMINU SABO
Kotun Musulunci a Jihar Kano ta tsare wasu mutum hudu a gidan yari kan zargin yin da shaye-shaye da kuma buga ludo a cikin wani masallaci.
Kotun Musulunci da ke unguwar PRP a Gama a Karamar Hukumar Nassarawa ta ba da umarnin ne bayan an gurfanar da mutanen wadanda duk mazauna unguwar Rimin Kebe ne.
Zazzabin Dengue ya bullo a jihar Sokoto mutum 13 sun kamu -Hukumar NCDC
Aminiya ta ruwaito cewa Auwalu Usman ne ya yi karar cewa mutanen hudu sun hada baki suna shiga masallaci domin yin wasan ludo da kuma shaye-shaye.
Ya ce yayin da ya yi yunkurin hana su, sai suka taru suka yi masa dukan tsiya tare da yi masa barazana cewa ya yi musu katsa-landan a harkokinsu.
Wanda ake kara na farko ya amince da laifin da ake tuhumar sa, yayin da sauran ukun suka musanta zargin da ake yi musu a lokacin da mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanta musu tuhume-tuhumen.
Alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2024, domin gabatar da shaidu a gaban kotu.
A wani labarin kuma Zazzabin Dengue ya bullo a jihar Sokoto mutum 13 sun kamu -Hukumar NCDC
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
