News
Zazzabin Dengue ya bullo a jihar Sokoto mutum 13 sun kamu -Hukumar NCDC
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC a ranar Asabar ta bayyana cewa zazzabin Dengue ya bullo a jihar Sokoto.
Shugaban hukumar Ifedayo Adetifa ya ce cutar ta fara bullowar a jihar tun a watar Nuwamba.
Adetifa ya ce zuwa yanzu ana zaton mutum 71 sun kamu da cutar amma an samu tabbacin mutum 13 da suka kamu da cutar a kananan hukumomi uku a jihar.
Ya ce hukumar ta samu rahotan cewa mutum 69 sun kamu da cutar a karamar hukumar Sokoto ta Kudu, mutum uku a Wamako sannan mutum daya a Dange Shuni.
Premium Times ta ruwaito cewa Zuwa yanzu babu wanda cutar ta kashe.
“Da dama daga cikin yawan da ake zargin sun kamu da yawan da suka kamu da cutar na da shekaru 21 zuwa 40.
Adetifa ya ce akwai isassun jami’an lafiyan da za su iya kula da mutane tare da yakan cutar a kasar nan.
Ya ce gwamnati ta bude wurin gwajin cutar da kula da wadanda suka kamu da cutar a babban asibitin Usman Dan Fodio dake jihar Sokoto.
MZazzabin Dengue
Zazzabin Dengue cuta ce da ake kamuwa da ita idan sauron dake dauke da kwayoyin ‘Dengue Virus’ ya ciji mutum.
Zuwa yanzu babu tabbacin ko mutum na iya kamuwa da cutar daga jikin wanda ke dauke da cutar amma wanda ya kamu da cutar idan ya warke zai iya kara kamuwa da cutar idan har bai dauki matakan kare kansa ba.
Mutum na iya warkewa cikin mako daya zuwa biyu bayan kamuwa da cutar sannan cutar na iya yi ajalin mutum idan har ba a sha magani ba.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, ciwon ido, ciwon gabobin jiki, amai, kumburin mukamiki da kurarraji.
