Connect with us

News

Kotu ta haramta wa Donald Trump tsayawa takara a 2024

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Kotun ƙoli a jihar Colorado ta Amurka ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump bai cancanci tsayawa takara ba kuma ba zai iya fitowa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar Republican a shekara mai zuwa ba.

 

Kotun ta ce saboda abin da tsohon shugaban ya yi a ranar 6 ga Janairun 2021 – ranar da aka kai hari kan ginin majalisa – Capitol hill – da aka yi wa kallon yunƙurin tayar da zaune tsaye.

Masu shayi koko da kosai na zabga ciniki a garin Kano a dalilin yanayi na hunturu da aka shiga.

Bbc ta ruwaito cewa Ofishin yaƙin neman zaben Trump ya kira hukuncin kotun a matsayin abin da ya saɓawa dimokradiyya, sannan kuma ya ce zai ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙolin tarayya.

Advertisement

Za a jingine hukuncin har sai kotun tarayya ta yanke nata, to amma duk da haka jami’an zaɓe a Colorado sun ce akwai buƙatar a yi abin da ya dace kafin nan da 5 ga watan Janairun 2024.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending