News
Babu Tanadin Aikin Kidiyar ‘Yan Najeriya A Cikin Kasafin Kudin 2024 – Majalissa

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Alamu na nuni da cewa babu wani tanadi da aka tsara na kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2024 a cikin kudirin kasafin kudin 2024 na hukumar kidaya ta kasa.
Mambobin kwamitin majalisar dattijai kan kasafin kudi sun kadu a ranar Talata lokacin da aka sanar da halin da ake ciki.
Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan kidaya, Sanata Abdul Ningi, ya sanar da ‘yan majalisar game da al’amarin a lokacin da yake gabatar da rahoton kasafin kudin hukumar kidaya na shekarar 2024 ga kwamitin tattara bayanai.
Ya shaida wa kwamitin cewa idan ba a samar da kudin kidayar a cikin kasafin kudin kasa ba, kasar nan za ta yi asarar kusan Naira billiyan 200 da hukumar kidaya ta kasa ta kashe wajen aikin kawo yanzu.
Sai dai ya bayyanawa kwamitin cewa hukumar za ta bayyana yau Laraba tare da bayanan nawa suke bukata don gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2024.
A wani labarin kuma Bai Kamata Gwamnatin Jihar Kano Ta Ɗauki Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi Ta Gina Gadoji A Birni Ba -Abba Hikima
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
