News
Diyar Dala 15,400: Dalibai sun shigar da ƙara bayan an rage daƙiƙa 90 cikin lokacin jarabawa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ɗaliban koriya ta kudu sun shigar ƙara kan gwamnati bisa tuhumar tsayar da jarabawar shiga kwaleji daƙiƙa 90 kafin lokacin da aka tsara musu
Sun buƙaci a biya kowannensu dala15,400 , wanda shi ne kuɗin karatun sake ɗaukar jarabaewar
kuskuren ya shafi jarabawar sauran ɗaliban a cewar lauya+nsu
Jarabawar shiga kwaleji ta ƙasa wanda, da ake kira Suneung , jarabawa ce da ake kwashe tsawon awa takwas ana yi ba tare da tsagaitawa ko hutu ba inda a ke rubuta darussa masu yawa.
Suneung na daya daga cikin jarabawa mafi wahala a duniya
Amfaninta bai tsaya iya wajen tantance gurbin jami’a da wajen aiki ba, ta na da tasiri akan mu’amalar rayuwa. An saka matakai domin taimakawa daliɓai wajen mai da hankali a lokacin jarabawar da ake yi shekara shekara kamar rufe sararin samaniya da kuma jinkirta buɗe kasuwar hannun jari
An fitar sakamakon jarabawar na wannan shekarar a ranar 8 ga watan disamba.
Bbc ta ruwaito cewa A cikin ƙarar da aƙalla ɗalibai 39 suka shigar a ranar talata, sun yi iƙirarin cewa an buga ƙararrawa a wani wurin gudanar da jarabawar da ke babban birnin ƙasar Seoul a lokacin darasin harshe Korean wanda shine darasin farko a jarabawar.
