Connect with us

News

Jam’iyyun APC da NNPP Sun Koma Ga Allah Yayin Da Kotun Koli Zata Fara Sauraren Karar Zaben Gwamnan Jihar 

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Manyan jam’iyyun siyasar Kano biyu sun koma ga Allah, a daidai lokacin da kotun koli zata fara sauraren karar zaben gwamnan Jihar kano

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Kotun koli ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamba domin sauraren karar zaben gwamnan Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 437.3.

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun fara sauraren karar zaben gwamnan Jihar kano

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

 

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

 

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending